Sojojin rundunar Operation Desert Sanity II sun kashe kwamandan masana’antar kera ababen fashewa na kungiyar ISWAP, Malam Muhammad, a Dajin Sambisa.
Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun aika Muhammadu lahira ne a wani kazamin gumurzu a ranar 14 ga watan Mayu a sansanin ’yan ta’addan a Ukuba da Njimia a Karamar Hukumar Bama.
Kamar yadda zagazola makama masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi ke cewa, Malam Muhammadu ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya jagoranci wani taron bitar ISWAP kan kirkire-kirkiren abubuwan fashewa.
Suna cikin taron ne sojoji suka rutsa shi da mayakan kungiyar ne suka aika su lahira.
- Kona masallaci: Yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 10
- An kashe matashi saboda bacewar hula a Bauchi
Muhammadu ya sha aika kananan yara su kai harin kunar bakin wake ta hanyar tayar da bama-bamai, ciki har da ’ya’yansa uku.
Wasu majiyoyin leken asiri sun kara shaida wa Zagazola Makama cewa sojojin sun kuma kama wata mota dauke da bama-baman da aka kera domin kai wa sojoji hari da ita.