Dakarun sojan Najeriya daga runduar ‘Operation Hadin Kai’ (OPHK) sun cafke wasu mutum 13 da ke sayar wa mayakan ISWAP kayayyakin da suke amfani da su a hare-haren da suke kai wa al’umomi a Jihar Borno.
Rahotanni daga yankin tafkin Chadi na cewa an kama mutanen ne ranar Talata yayin wani samame da dakarun Najeriya da na Civilian JTF suka kai kasuwar Benishek a Karamar Hukumar Kaga cikin jihar.
- Barazanar kisa: Kotu ta sa a cafke shugaban APC na Kano
- Atiku zai bude makarantar haddar Al-Kur’ani mai dalibai 500 a Kano
Wata majiya yankin ta ce, “A duk ranar kasuwa, ’yan kasuwa da ke wa mayakan ISWAP aiki kan tafi kasuwanni domin sayo musu kayayyakin abinci da man fetur da layukan salula da kayan sanyawa da sauran kayayyain da suke bukata.”
Rahoton ya ce an kama su ne yayin da suke kokarin fitar da man fetur mai yawa da abinci zuwa wurin da mayakan ISWAP suke.