Dakarun rundunar Operation Hadin Kai da na MNJTF sun cafke wani mai shekara 45, Aji Dala, da ke Karamar Hukumar Monguno, bisa zargin fallasa bayanansu ga ’yan ta’addan ISWAP.
A cewar Zagazola Makama, kwararren masani akan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, dakarun bataliya ta 242 su ne suka kama wanda ake zargin tare da hadin gwiwar jami’an leken asiri a yankin Charamari na garin a ranar 14 ga Nuwamba, 2023.
- Hatsarin kwalekwale ya yi ajalin mutum 10 a Neja
- Dan PDP daya tilo a Majalisar Dokokin Yobe ya koma APC
Ya ce sun gano a cikin wata wasika da Aji Dala ke dauke da ita kan ’yan ta’adda a kan shirin su na kai hari a garin Monguno a ranar 17 ga Nuwamba, 2023.
Kamar yadda majiyar ta nuna, wasikar dai na dauke ne da sa hannun Amir Hallat Muhammed na Kungiyar ta ISWAP.
Sakon da ke dauke a wasikar na nuna cewar, “Ya kamata a shirya mutanen Monguno. Mu (ISWAP) muna zuwa ne don mu kawo muku hari ranar Laraba.”
Zagazola ya fahimci cewa sakon wanda ake zargin ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin na Monguno, duk da cewa daga baya an gano cewa bangaren na ISWAP din ne suka turo shi da sakon da ya haifar da firgicin.
Kazalika, wata majiyar soji na kara nuna cewar rundunar sojan Najeriya ta yi kira ga al’ummar yankin da su yi watsi da fargabar da suke yi na yiwuwar kawo harin da ’yan ta’addan ke shirin yi, inda ta ce sojojin a shirye suke su tunkari duk wata barazana da ka iya tasowa.