Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, tana gudanar da bincike kan wani dukan kawo wuƙa da wasu matasa suka yi wa waɗansu mutane su biyu da ake zargi da satar kare a unguwar Lushi da ke cikin garin Bauchi.
Dukan da ya yi sanadin rasa ran ɗaya daga cikinsu mai suna Peter.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar da haka ga manema labarai a Bauchi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata kan wani mutum mai suna Peter a ranar 9 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare.
Wakil ya ce waɗanda ake zargi Dokagk Danladi mai shekara 38 da kuma Peter matasan sun musu duka ne sakamakon zargin da ake musu.
Ya ce, “Dokagk ya samu munanan raunuka da suka haɗa da raunukan sara da adda a kansa, kuma tuni aka kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi domin kula da lafiyarsa, an gano abokin nasa Peter, wanda har yanzu ba a san sunan babansa ba, a wurin da lamarin ya faru, abin takaici ma’aikatan lafiya sun bayyana cewa shi peter ya mutu.”
A halin yanzu ana gudanar da bincike. Rundunar tana aiki tuƙuru don ganin an gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari, tare da maida hankali wajen zaƙulo duk waɗanda ke da hannu a lamarin.
Wakil ya ce babban Jami’in ’yan sanda da ke kula da shiyyar Yalwa (DPO) yana jagorantar tawagar masu binciken waɗanda suka ziyarci wurin da laifin da ya faru don tattara shaida da samun cikakken bayanai kan lamarin .
Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce, Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu ya bayyana wannan aika-aika a matsayin “wata ɓarna da kuma illa ga tsarin dokokin ƙasarmu”.
“Ya kuma gargaɗi ’yan asalin Jihar Bauchi cewa, a ƙarƙashin shugabancinsa rundunar ba za ta lamunci duk wani mutum da ke ɗaukar doka a hannunsu ta hanyar cutar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan da suka saɓa wa doka ba.
“Ya ƙara jaddada cewa, babu wani mutum da ke da hurumin mu’amala da wanda ake tuhuma ta hanyar da ba ta dace ba, kuma hakan ba daidai ba ne ga kowa ya ɗauki nauyin aiwatar da doka. Ya kamata a gaggauta miƙa waɗanda ake zargi da aikata laifin da ake tuhuma ga ‘yan sanda ko hukumomin da abin ya shafa da ke da alhakin bincike da gurfanar da su a gaban kotu.”
Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da bincike.