✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan PDP daya tilo a Majalisar Dokokin Yobe ya koma APC

Dam majalisar dai shi ne ya kayar da tsohon Kakakin majalisar Jihar

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karbi bakuncin Lawan Musa Majakura, dan jam’iyyar PDP daya tilo a Majalisar Dokokin Jihar wanda ya canza sheka ya zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Jihar.

Gwamnan ya bayyana Majakura a matsayin matashi kuma hazikin dan siyasa mai kima a idon jama’arsa.

A cewar Gwamnan, “Siyasa ita ce hidima ga jama’a, na gamsu da jajircewar ka na yi wa mazabarka hidima yadda ya kamata.

“Na kuma gamsu da irin kimar mutanen da ke rako ka zuwa wannan taron, hakan ya nuna karbuwarka daga wannan rukunin ’yan siyasa masu sahihanci,” in ji Gwamna Buni.

Tun da farko, a jawabinsa Hon.  Lawan Musa Majakura ya ce ya gamsu da canza Sheka daga  jam’iyyar PDP zuwa APC saboda irin namijin kokarin da gwamnatin Buni ta ke yi na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar mazabar sa.

Ya ce gine-ginen tituna, gidaje, wuraren kiwon lafiya, da sauran su ya kawo sauyi ga al’umma a mazabarsa.

“Ina so in hada kai da ku domin wajen yi wa mazabata hidima domin inganta rayuwar al’ummata kamar yadda bukatar al’ummar mazaba suka bukata.

“Na tabbata za mu iya samun nasarori idan har na kasance tare da ku a cikin jam’iyyar APC, zai fi amfani ga al’ummar mazabata,” in ji Majakura.

Shima da yake jawabi, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Chiroma Buba Mashio, ya bayyana dan majalisar a matsayin wanda ya yi fice wajen kare muradun jama’ar sa.

“Hon. Lawan Musa Majakura ya nuna jajircewarsa wajen kare muradun al’ummarsa a zauren majalisar.

“Komawarsa APC wata fa’ida ce ga jam’iyyar da kuma gwamnatin jihar Yobe,” in ji Kakakin na majalisar.

Idan za a iya tunawa, matashin dan majalisar mai shekara 29 shi ne ya kayar da tsohon Kakakin Majalisar a zaben da ya gudana a watan Maris.

%d bloggers like this: