✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato

An samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin.

Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace.

 Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan.

Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin.

Sai dai a baya, Danjuma Auta, babban sakataren ƙungiyar raya Irigwe (IDA), ya musanta batun satar shanu a yankin, yana mai zargin cewa an kashe mambobinsu da dama a cikin makonni uku da suka gabata, kuma suna fuskantar ƙalubale na hare-hare.

A cewar Ya’u Idris, shugaban Ƙungiyar MACBAN a garin Bassa, wanda ya tabbatar da samun nasarar gano gawar makiyayin da ya ɓace, sojojin OPSH tare da wasu makiyaya ne suka tsinto gawar a wani kabari mara zurfi, tare da wasu makiyaya a gaɓar kogi da ke kusa da babban yankin Ariri.

Ya ce, an fille kan makiyayin, aka datse hannunsa na hagu.

Da yake ƙarin bayani, shugaban ya ce, “Mun tono gawar kuma muka mayar da shi gida don yin sallar jana’iza, an ceto sama da kashi 80% na shanun, muna godiya ga jami’an tsaro musamman jami’an tsaron OPSH bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ƙwato gawar da shanu.”

Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da DSP Alabo Alfred na rundunar ’yan sandan jihar, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu kan wannan lamari ba.