Dakarun runduna ta 82 ta Sojin Kasa na Najeriya sun kama Godwin Nnamdi, wani jagoran haramtacciyar kungiyar ’yan aware ta IPOB a Jihar Enugu.
Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarun rundunar Operation Golden Dawn ne suka kama wanda ake zargin a ranar Kirsimeti.
- Taliban ta haramta wa Mata balaguro ba muharrami
- Hadarin mota ya kashe ’yan Najeriya 14,773 a cikin shekaru 3
Janar Nwachukwu ya ce an kama shugaban kungiyar yayin wani samame da suka kai Karamar Hukumar Nkanu ta Gabas a Enugu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Janar Nwachukwu yana cewa sojojin sun kwace wata bindiga guda daya kirar AK-47 da harsasai da kuma wayar salula daga hannun Godwin Nnamdi.
“An kama jagoran IPOB yayin wani samame a wani sansani da ake zargin shi ne matsugunin kungiyar a Dajin Akpowfu da ke Karamar Hukumar Nkanu ta Gabas,” in ji shi.
“A yayin samamen da sojojin suka kai, sun yi artabu da wasu ’yan awaren wanda hakan ya tilasta musu arcewa kuma aka samu nasarar kama jagoransu.
“Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya yayin da yake yaba wa bajintar sojojin, ya umarci da su bankado duk wata maboya da ke tsugunar da yan taadda a yankun da ke karkashin nauyin da rataya a wuyansu,” a cewar Janar Nwachukwu.