✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB: Sojoji sun harbe mahara 4 a Imo

An kashe maharan yayin musayar wuta da dakarun soji.

Dakarun runduna ta 34 ta Sojojin Najeriya sun yi kashe wasu mahara hudu a ake zargin ’yan tawayen IPOB ne a yankunan Amaifeke da Ihioma na Karamar Hukumar Orlu ta Jihar Imo.

Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana wa manema labarai a Owerri cewa kayayyakin da aka kwato a yayin arangamar sun hada da bindiga daya da harsashi 10.

Sauran sun hada da wata mota kirar Toyota Hilux da aka gano maharan sun kwace ranar Lahadi da kuma wayoyin hannu da laya.

Nwachukwu ya bayyana cewa maharan wadanda ake zargin ’yan awaren Biyafara (IPOB) ne, an kashe su ne a wata arangama da suka yi da sojojin.

Ya ce an kashe su ne a lokacin da suke kokarin tilasta wa mutane zama a gida ta hanyar harbe-harbe da kuma barazana ga rayuka da dukiyoyin ’yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.

“Sun bude wuta ne a lokacin da suka ga masu sintiri sun fito domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.

“Rundunar da kama masu laifin tare da kashe hudu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere,” in ji shi.

Nwachukwu ya bukaci jama’a da su bayar da sahihan bayanai kan masu aikata laifuka ga jami’an tsaro a duk lokacin da aka gan su a cikin al’ummarsu.