Rundunar Sojin Najeriya, ta sanar da cewar dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da kama wasu 44 da suka miƙa wuya a Jihar Borno.
Wannan na ɗauke cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X (twitter), a ranar Talata.
- DAGA LARABA: Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda
- ’Yan Najeriya na mutuwa saboda manufofin Tinubu – Ɗan Bello
A yayin ayyukansu, sojojin sun gano abubuwa masu fashewa, makamai, alburusai, da shanun da aka sace, sannan sun kama wasu masu laifi.
Sojojin, sun bayyana cewa a ranar Litinin, sun kai hari sansanin ’yan ta’addan ISWAP da ke yankin Bama a Jihar Borno.
A wannan samame, sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da ƙwato wasu abubuwa kamar bam, RPG, bindigogi guda biyu, AK-47, alburusai 23, babura guda shida, da kuma wasu magunguna.
Kazalika, sojojin sun ce sakamakon ci gaba da kai hare-hare a yankin Arewa Maso Gabas, ’yan Boko Haram guda 44 da iyalansu sun miƙa wuya ga dakaru a yankunan Bama, Dikwa, da Gwoza na Jihar Borno.