Sojoji da ke karkashin rundunar tsaro ta Operation Thunder Strike a daren ranar Litinin sun hallak wasu ’yan bindiga guda biyu a kan hanyar Sabon Iche zuwa Kagarko da ke Karamar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Majiyoyi daga yankin sun ce ’yan bindigar na daga cikin wadanda suka addabi yankin suka kuma hana al’ummarsa sakat.
- Mazajen Kano sun koma lakada wa matansu dukan tsiya —Hisbah
- Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano
Kazalika, wasu rahotannin tsaro daga Gwamnatin Jihar Kaduna sun ce dakarun sun yi kwanton bauna ne a kan hanyar bayan samun wasu bayanan tsaro na sirri a kan zirga-zirgar ’yan bindigar a yankin.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce ’yan bindigar sun fada komar jami’an tsaron ne cikin rashin sani su kuma suka bude musu wuta, a daidai lokacin da suke kokarin tare hanyar domin yi ta’asa.
Daga nan ne su kuma suka yi kokarin mayar da martani, lamarin da ya janyo musayar wuta tare da kashe biyu daga cikinsu nan take, wasu kuma da dama suka tsere da munanan raunuka a jikinsu.
Sai dai ya ce jami’an tsaron sun sami nasarar dauko gawawwakin ’yan bindigar bayan ba-ta-kashin.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da su kai rahoton duk wani wanda ya zo da rauni a jikinsa don neman magani saboda zai iya kasancewa daya daga cikinsu.
Samuel ya ce, “Jama’a su fahimci cewa duk wanda aka samu yana kokarin bayar da magani a fakaice, ko yin jinya ga wadanda harsashi ya farfasawa jiki, shi ma za a yanke masa hukunci iri daya da su.”