Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe Maikusa, wani kasurgumin dan ta’adda da ke jagorantar hare-hare a Jihar Katsina.
Maikusa ne mataimakin wani fitaccen dan ta’addan da ya addabi jama’ar Jihar Katsina Modi Modi, wanda ake nema ruwa a jallo.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya, Manjo-Janar, Onyema Nwachukwu ne ya sanar cewa sojojin sun hallaka Maikusa da wasu ’yan ta’adda uku ne a ranar Litinin, a tsakanin kananan hukumomin Kurfi da Safana da ke jihar bayan bata kashin da sojin suka yi da ’yan ta’addan.
Ya ce, wannan gagarumin aiki ya yi nasarar kawar da ’yan ta’addar da suka jima suna addabar al’ummar yankunan.
- Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma
- EFCC ta kama motoci 21 maƙare da kayan abinci a hanyar fita ƙetare
A cewarsa, sojojin sun fuskanci turjiya daga ’yan ta’addar, amma dai sun yi galaba a kansu da karfin wuta, inda suka hallaka su, yayin da wasu suka tsere.
Ministan Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce sojoji a cikin ’yan watannin da suka gabata sun kashe akalla manyan jagororin ’yan tada kayar baya bakwai a kasar.
Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a Jaji ranar Talata.
Ministan wanda ya kai ziyarar aiki, ya gabatar da jawabi ga sojojin da ke halartar wani taron kara wa juna sani da kwalejin yaki da ta’addanci da ’yan ta’adda.