Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bayyana cewar dakarunta sun hallaka wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ta ke nema ruwa a jallo a Jihar Kaduna.
Rundunar, ta ce an hallaka shi ne yayin da yake tafiya da wasu muƙarrabansa, bayan wasu bayanan sirri da ta samu.
An yi artabu tsakanin maharan da dakarun sojin wanda hakan ya sa suka yi nasarar hallaka shi.
Kakakin rundunar, Air Vice Mashal Edward Gabkwet ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
Ya ce an kashe ɗan bindigar ne, Mustapha Abdullahi, tare da wasu mutum biyar daga cikin yaransa, bayan da aka samu bayanan sirri kan zirga-zirgarsu a kusa d dajin Sabon Gida, da ke kan hanyar Sabon Birni a ƙaramar hukumar Igabi a jihar.
“Bayan da aka tura jami’an sojin sama su bincike yankin, sun haɗu da ’yan bindigar a kan babura, inda suka yi musayar wuta da su, inda sojojin suka hallaka su gaba ɗaya.
Gabkwet, ya ce kayan da aka samu a wajen ’yan ta’addar sun haɗa da bindigar maharba guda biyar, da bindiga mai sarrafa kanta kirar gida.
Kazalika, ya ce an samu harsasai da layu da layukan waya da kuma rigar wayoyin hannu.
Wannan dai ma zuwa ne bayan yunƙurin da dakarun ke yi na kawo ƙarshen ayyukan mahara a yankin Arewa Maso Yamma.