✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno

Jiragen yakin rundunar tsaron hadin gwiwa ta kasa da kasa sun halaka mayakan kungiyar ISWAP da daman gaske tare da jikkata wasu da dama a Jihar Borno.…

Jiragen yakin rundunar tsaron hadin gwiwa ta kasa da kasa sun halaka mayakan kungiyar ISWAP da daman gaske tare da jikkata wasu da dama a Jihar Borno.

Rahotanni sun ce dakarun sun kai harin ne a garuruwan Sabon Tumbun da Jibularam, a Karamar Hukumar Marte da ke Arewa maso Gabashin Jihar Borno.

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa masanin harkokin tsaron nan Zagazola Makama cewa jiragen sun kai wa ’yan ta’addan hare-haren ne jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a sansanin su.

Majiyoyin sun ce an aiwatar da wannan hari ne bisa sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa ’yan kungiyar ta ISWAP na haduwa da yawa.

“Rahoton na nuna cewar lalle wadannan hare-hare da jiragen yakin na rundunar tsaron ta MNJTF suka rika kaiwa mayakan na ISWAP sun yi tasiri matuka kasancewar mayaka masu ikirarin jihadi da dama sun mutu, wasu kuma suka samu munanan raunuka.

“Ba za mu iya tantance ainihin adadin ’yan ta’addan da aka kashe ba, amma sun fi 12,’ inji majiyar tamu.

Rundunar ta MNJTF ta zafafa kai hare-hare domin kakkabe yankin Tumbuns gaba daya daga ayyukan ’yan ta’adda a karkashin Operation Lake Sanity, reshen Operation HADIN KAI.