Sojojin Najeriya sun yi wa wani gini kawanya, bisa zargin ana amfani da shi a matsayin sansanin kyankyasar jarirai da kuma safarar mutane a Jihar Adamawa.
Kwamandan runduna ta 23 da ke Yola, babban birnin Jihar, Birgediya Janar Mohammed Gambo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedkwatarsu ranar Litinin.
- Tinubu ya sanya wa filin jirgin saman Maiduguri sunan Buhari
- Shugaban NUC ya ajiye mukaminsa, zai koma koyarwa a BUK
Ya kuma ce a sakamakon samamen, sun kuma samu nasarar kama mutum bakwai a sansasnin.
Ya ce sun gano wajen ne lokacin da dakarunsu ke kan wani aikin sintiri na musamman a kan iyakar Najeriya da Kamaru, lokacin da suka samu ingantattun bayanan sirri kan ayyukan batagarin.
Birgediya Mohammed ya ce lokacin da suka yi kamen, akwai ’yan mata 17 masu tsakanin shekara 19 zuwa 21, wadanda suka kasance a sansanin na tsawon shekara 2 zuwa uku, ba tare da sanin iyayensu ba.
Ya lura cewa gano sansanin ya dada nuna damuwar da ake da ita kan matsalar safarar mutane a Najeriya.
Daga nan sai Kwamandan ya yaba wa hobbasan sojojin wajen ganowa tare da yin abin da ya dace da sansanin, inda ya ce hakan babbar nasara ce ga aikin kakkabe safarar mutane a Najeriya.