An shiga ruɗani bayan da wasu sojoji sun lakaɗa wa wasu ’yan sanda da ke bakin aiki duka a Ƙaramar Hukumar Okpe da ke Jihar Delta.
Rikicin jami’an tsaron ya samo asali ne bayan ’yan sanda sun yi kamen wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.
’Yan sanda sun tsare motar matasan ne a yayin wani samame, inda suka kama ɗaya daga cikinsu da loud da wiwi, bayan sauran sun tsere.
Suna tsaka da tafiya da shi zuwa ofis ne suka bi ta wani shigen bincike na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, suka umarce su da su sake shi.
Bayan ’yan sandan sun ƙi amincewa suka nemi a bi ƙa’ida ba ne, rikici ya ɓarke a tsakaninsu. A garin haka ne sojojin suka lakaɗa wa ’yan sandan duka.
Kakakin ’yan sandan Jihar Delta, SP Edafe Bright, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da cin mutunci, mara dalili.
Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki cikin kyakkyawan alaƙa da sauran hukumomin tsaro.
Jami’in ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike a kan lamarin da nufin ɗaukar mataki da nufin daƙile aukuwar hakan a nan gaba.
Yunƙurin wakilinmu na jin ta bakin rundunar Sojin sama kan lamarin bai yi nasara ba.
Al’ummar gari dai sun bayyana buƙatar sun bukaci jami’an tsaron su kai zuciya nesa tare da kyautata hulɗa a tsakaninsu.