Dakarun sojin Najeriya sun kubutar da wasu mutun 30 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
A cewar wata sanarwa da Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar sojin, Laftanar-Kanar Musa Yahaya, sojojin sun yi artabu da ’yan bindigar da suka sace matafiya a kauyen Manini da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
- Kano ta Tsakiya: Kotun Koli ta tabbatar da takarar Laila Buhari
- Babu wanda nake tsoro —El-Rufai ga ‘’yan fadar Buhari’
Sojojin da ke rakiyar Babban Kwamandan Tsaro da Ayyuka, Manjo-Janar SE Udonwa, wanda ya kai ziyarar aiki a hedikwatar ‘Operation Whirl Punch’ da ke Birnin Gwari, sun yi galaba a kan ’yan bindigar ne a yayin wani artabu da suka yi, wanda hakan ya sa ’yan ta’addan suka tsere suka bar makamansu.
Yayin artabun, sojojin sun yi nasarar ceto mutum 30 da maharan suka sace, tare da kwato babura guda biyu, kuma nan take suka sake bude babbar hanyar domin zirga-zirgar ababen hawa.
Kazalika sun raka wadanda suka ceto zuwa yankin Udawa da Birnin Gwari don komawa muhallansu.
Sanarwar ta kara da cewa, “Manjo-Janar SE Udonwa, ya yaba wa sojojin saboda kwarewar da suka nuna wajen ceto wadanda abun ya rutsa da su.”
Jami’an tsaro na ci gaba da samun galaba a kan ’yan bindiga da suka addabi Jihar Kaduna da kewaye.