Gwamnatin jihar Kaduna ta ce rundunar tsaro ta ‘Operation Safe Haven’ (OPSH) ta dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Gidan Zaki da ke Karamar Hukumar Zangon–Kataf a Jihar.
Kwamishinan Tsaron da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Lahadi.
Ya ce, “Yayin harin, ’yan bindigar sun lalata gidan wani mazaunin kauyen.
“Sun kuma lalata wata motar da ke kusa da wani shagon cajin waya na wani mutum, sannan suka kwashe wayoyin mutane da aka kawo caji,’’ inji shi.
A cewar Kwamishinan, saurin kai daukin da sojojin suka yi ya sanya ’yan bindigar tserewa.
Aruwan ya kara da cewar sai dai wata mata ta ji rauni sakamakon harin ’yan bindigar.
“Wata mazauniyar kauyen ta samu rauni sakamakon harsashin da suka harba a lokacin da suke harbe-harbe.
“An garzaya da ita ta zuwa wani asibiti da ke kusa don kula da ita.”
Kwamishinan ya kuma ce Gwamna jihar, Nasir El-Rufai ya samu rahoton faruwar lamarin, sannan ya jinjinawa sojojin kan namijin kokarin da suka yi na dakile maharan.
Shima kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ya faru ne da misalin karfe uku na daren ranar Lahadi.