Dakarun sojoijn Najeriya sun dakile wani hari da mayakan kungiyar ISWAP suka kai wa masu zabe a garin Damboa da ke Karamar Hukumar Damboa a Jihar Borno.
Mayakan sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 10 na safe a yayin da ake tsaka da zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha a ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.
- Gobara ta tashi a Kasuwar Gamboru da ke Maiduguri
- ’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wurin zabe
Majiyarmu ta ce, “Duk da cewa mayakan sun yi ta harbi bama-bamai, an yi nasarar daidaita al’amura daga baya, an ci gaba da yin zabe.”
Majiyar ta ce cikin gaggawa sojoji suka amsa kiran neman dauki da aka yi musu kuma sun yi nasarar dawo da komai yadda yake a garin, kuma an ci gaba da harkokin zabe.
Wakilinmu ya yi yunkurin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Borno, Sani Kamilu Shatambaya, amma hakar ba ta cimma ruwa ba, bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka tura masa.
Sagir Kano Saleh; Hamisu Kabir Matazu da Olatunji Omirin, Maiduguri