✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutum 30 da aka sace a Nasarawa

An ceto mutum 30 da aka sace a yankuna da daban-daban.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ceto wasu mutum 30 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Nasarawa.

Lamarin na zuwa ne yayin da rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ ta fafata da ’yan bindigar a yankin Idu, Chikara da ke iyaka da Karamar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa da kuma Abaji da Koton Karfe a Jihar Kogi.

Mataimakin Daraktan rundunar sojin, Kyaftin Godfrey Abaakpa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Ya ce sojojin sun gudanar kai farmakin ne tare da rundunar hadin gwiwa ta CJTF a Jihar Nassarawa

Abakpa ya ce sojojin sun fatattaki ’yan bindigar tare da kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu da dama suka tsere.

Ya kara da cewa sojojin sun kuma kashe ’yan bindiga biyu.

A cewarsa, wani jami’in tsaro daya ya samu rauni a arangamar wanda kuma a yanzu yana asibiti yana jinya.

“Sojoji sun kuma samu nasarar kwato makamai daga hannun ’yan ta’addan da kakin sojoji da dama.

“Rundunar ’yan sandan Najeriya da ke Karamar Hukumar Toto ta bayyana sunayen mutanen da aka ceto yayin da gwamnatin jihar ta taimaka musu wajen mika su ga iyalansu.

“Sojoji za su ci gaba da jajircewa kuma za su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin kawar da ’yan ta’adda a babban birnin tarayya, Abuja da kewaye da duk wasu masu aikata miyagun laifuka,” in ji shi.