✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutane 13 da aka sace a ƙauyen Kaduna

Sojoji sun ceto mutane 13 da aka sace bayan wani artabu da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Sojoji sun ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su bayan wani artabu da ’yan bindiga a kauyen Chigbolu da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Sun kuma kama wasu mutum uku da ke yi wa ’yan bindiga safarar makamai da kuma leken asiri a ƙaramar hukumar.

Sojoji sun kama mutanen ne da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da harsasai 121 da tsabar kudi ₦4,079,000.00.

A baya an ruwaito cewa ’yan bindiga sun sace mutane 13 a gonakinsu a yankin Chigbolu makonni biyu da suka gabata.

Wani shugaban al’ummar wanda ya bayyana hakan ta wayar tarho ga wakilinmu a ranar Lahadi, ya ce sojojin sun yi galaba a kan ’yan bindigar wanda hakan ya tilasta musu barin wadanda suka yi garkuwa da su suka gudu.

Wata majiyar jami’an tsaro, wacce ke cikin aikin, amma ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce, “An yi gumurzu sosai a yankin, inda aka ceto mutane 13 da lamarin ya rutsa da su, wadanda suka hada da maza shida da mata bakwai a ranar Alhamis.”

Ya ce an kwato bindigar ƙirar AK-47 guda daya, da ƙirar gida gida da kuma tsabar kuɗi Naira 192,220, da wayoyin hannu guda biyar a sansanin ’yan fashin.

A ranar Alhamis ɗin kuma sojoji sun kama wasu ’yan fashin guda biyu a kasuwar kauyen SCC.

Wakikinmu bai samu damar jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba kan lamarin.