Sojojin Najeriya sun ceto wata ma’aikaciyar agaji Grace Taku, bayan ta ta shafe shekara hudu a hannun mayakan kungiyar ISWAP.
A safiyar Asabar wata majiyar tsaro ta shaida mana cewa ana duba lafiyar Grace a asibitin sojoji na Maimalari da ke Maiduguri, bayan an ceto ta.
Majiyar ta ce sojojin sun “An ceto ta a galabaice, amma cikin hankalinta,” a wani samame a maboyar mayakan ISWAP.
Grace, ma’aikaciyar kungiar agaji ta Action Against Hunger (ACH)ce, kuma wata abokiyar aikinta ta tabbatar wa wakilinmu cewa sun kai mata ziyara a asibitin sojojin.
- Karin kudin tikiti: Za a dauki Dala 100 daga guzurin alhazai
- Baffa Hotoro ya nemi afuwar Sheikh Dahiru Bauchi a hannun DSS
Jami’ar ta ce, “Mun ji dadin ganin ta bayan shekara uku da wata 10 a hannun ISWAP. Na yi kuka sosai da na gan ta. Allah mai iko!
“Mun samu labari cewa sojoji sun ceto ne a 13 ga watan Mayu, 2023, Allah Ya saka wa sojojin rundunar Operation Hadin Kai da alheri.”
Wata majiyar ta ce kungiyar ISWAP ta sayar da Grace a matsayin baiwa, bayan rashin daidaitawa a tattaunawar kungiyar da Gwamnatin Tarayya a 2021.
A watan Yulin 2019 ne mayakan ISWAP suka yi garkuwa da Grace Taku da abokan aikinta biyar a yankin Damasak na Jihar Borno.
Kungiyar ta kashe sauran ta abokan aikin Grace su biyar, domin nuna fushinsu kan rashin samun biyan bukatunta daga gwamnati da jami’an tsaro.