Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Manjo-Janar Ibrahim Ali, ya ce an ceto wata Dalibar Makarantar Chibok da ’ya’ya mata uku daga hannun kungiyar Boko Haram.
Saratu Dauda mai shekaru 25, sojojin sun ceto ta ne a ranar 6 ga Mayu, 2023 a maboyar ’yan ta’addan a Ukuba dake Dajin Sambisa, jihar Borno.
- Bam Ya Kashe Sojoji 3, Ya Raunata 10 a harin ISWAP
- Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a kasar waje
Da yake mika Saratu ga kwamishinar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Zuwaira Gambo, a ranar Litinin a Maiduguri, Janar Ali, ya bayyana cewa: “Kafin a cece ta, Saratu ta auri Abu Yusuf, wani wanda bom ya tarwatse da shi, wanda masanin abubuwan fashewa ne na kungiyar ta Boko Haram.”
Ya ce ceto ta ke da wuya aka garzaya da ita asibitin sojoji na Maimalari domin samun kulawa ta musamman kafin ta mika ta da yaran nata uku ga gwamnatin jihar.
Cikin jawabinsa ya ce, “Mun gode wa Allah da Ya cece ku da ’ya’yanku. Wannan zai ba ku damar samun ingantacciyar rayuwa tare da ’ya’yanku da sauran iyalai a yankin Chibok.”
Ya ce daga cikin ’yan mata 276 da aka sace a ranar 14 ga Afrilu, 2014, 76 sun tsere, yayin da 107 Boko Haram suka sako su a shekarar 2018.
Sojoji sun kubutar da 186, amma har yanzu ‘yan mata 93 da aka sace suna hannun maharan.
Da take mayar da martani, Hajiya Zuwaira, ta ce Saratu da ’ya’yanta, gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kammala karatunsu na sakandare da jami’a a jihar.