✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bam Ya Kashe Sojoji 3, Ya Raunata 10 a harin ISWAP

Wata mota makare da bama-bamai da 'yan ta'addar kungiyar ISWAP suka tayar ta kashe sojoji uku a jihar Borno.

Wata mota makare da bama-bamai da ‘yan ta’addar kungiyar ISWAP suka tayar ta kashe sojoji uku a jihar Borno.

Wasu sojoji 10 kuma sun samu rauni a harin na ranar 14 ga Mayu, 2023, a yayin da sojojin suke ci gaba da kai samame kan sansanin ISWAP da ke yankin Tunbum Reza.

Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun mayar da martani inda suka kashe ’yan ta’addan da dama.

A cewarsa, motar da ke makare da bam din ta ci karo ne da wata mota yaki ta sojojin Najeriya, wadda wata motar kirar Hilux ke biye da ita.

Wata majiyar soji a Maiduguri ta ce ‘yan ta’addan sun yi asarar dimbin mayaka, duk da cewa ba a tabbatar da adadinsu ba ya zuwa yanzu.

Makama ya ce: “Wannan harin ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan sojoji sun dakile wani hari a Arege, inda kashe ‘yan ta’adda 10 tare da lalata motocinsu uku.

“Sun yi wani gagarumin yunƙuri na kutsa wa sojojin da ke gaba ta hanyar amfani da bama-bamai da aka tayar da su a cikin mota, amma nan take aka kashe su.”

Ya kara da cewa, an kwashi dakarun da suka samu raunuka zuwa wani asibitin sojoji da ke Maiduguri domin yi musu magani.