Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin horas da ‘yan sanda na PMFTC da ke Limankara, a Gwoza, inda suka kashe Sufeton ’yan sanda guda ɗaya.
Sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, yayin da jami’an tsaro suka fita sintiri a ƙafa.
- Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu
- An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu
Sufeto Andrawus Musa daga rundunar 6PMF da ke Maiduguri ya samu rauni a harin, inda maharan suka ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47.
An kai shi asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), amma rai ya yi halinsa.
Rundunar dai na gudanar da bincike kan hari, tare da ƙoƙarin ganin ta kama waɗanda suka kai hari.
Ta kuma nemi jama’a da suke sanya ido kan duk wani abun zargi, tare da bai wa jami’an tsaro rahoto.