Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wata yarinya ’yar shekara 15 bisa zargin jefa gawar wani jariri a cikin wani banɗaki da ke sansanin ’yan gudun hijira a Monguno.
A cewar wata majiyar ’yan sanda a ranar 22 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:15 na safe, an bayar da rahoton cewa, a safiyar wannan rana da misalin ƙarfe 6:00 na safe, an tsinci gawar wani jariri da aka haifa a yashe a ɗaya daga cikin banɗaki da ke sansanin.
- Kotu ta bai wa EFCC izinin binciken sayar da filin musabaƙar Alƙur’ani na N3.5bn a Kano
- Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno
Majiyar ta ce, wacce ake zargin mai suna Yafalmata Alhaji Mustapha mai shekara 15, da ke da zama a sansanin, a yanzu haka tana hannun ’yan sanda domin bincike.
“‘Yan sanda da ƙwararrun likitoci sun ziyarci wurin kuma an kai gawar jaririn zuwa babban asibitin Monguno. Likitan ya tabbatar da mutuwar jaririn da isarsa, kuma an ajiye gawar a asibiti domin a duba.” in ji majiyar.
Bayan binciken gawar an miwa ta ga shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Charamari domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.