An ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya.
Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna.
- Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani
- Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD
Abubakar ya ce baya ga horaswar da kwarrarru da aka dauko za su yi, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu.
Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su ci gajiyar wannan horaswar, yayin da daga bisani wasu 800 kuma su biyo baya.
Badaru ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin tunkarar matsalar ’yan ta’adda waɗanda su ma ke sauya dabaru a kodayaushe.
Kodayake ministan bai sanar da sunayen ƙasashen da za a ɗauka hayar waɗannan zaratan sojojin ba, amma ya ce za a ɗauko su ne daga wasu ƙasashen duniya bakwai.
A zangon farko kaɗai, jimillar sojojin Nijeriya dubu 2 da 400 ne za a fara bai wa horan na musamman, kafin a tsallaka zuwa zango na biyu.
Ministan ya bayyana cewa, ana samun kwanciyar hankali a wasu yankunan ƙasar sakamakon yadda gwamnati ta duƙufa wajen magance matsalar tsaro, inda har ya ba da misali da yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, yankin da a cewarsa, an samu zaman lafiya a yanzu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar ’yan bindiga musamman a yankin arewacin Najeriya, inda suke garkuwa da jama’a domin karɓar kuɗin fansa, yayin da a wasu lokuta suke aiwatar da kisa.