✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang

Gwamnan ya ce bai kamata a ce har ƙungiyoyin 'yan ta'adda sun yi ƙarfi haka a Najeriya ba.

Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi.

Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro.

Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida.

“Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da ke iya ƙalubalantar hukumomin tsaronmu,” in ji Mutfwang.

“Najeriya ba za ta sake yin kuskuren barin ‘yan ta’adda su sake yin irin wannan ƙarfi ba.”

Ya yaba wa sojoji kan ƙoƙarinsu na inganta tsaro a Jihar Filato: “Saboda amfani da fasaha da ƙoƙarin jami’an tsaro, Filato ta fara dawo da sunanta a matsayin waje mai zaman lafiya da yawon buɗe ido.”