Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa ta samu nasarar damke wasu mutane tara wadanda ake zargin suna hannu a sacewa tare da kisan gillar da aka yi wa dan Majalisar Dokoki na Jihar Taraba, Hon. Hosea Ibbi.
A yayin samamen, wadda runduna ta 23 ta sojin tare da hadin gwiwar sashen jami’an DSS suka shirya mai taken ‘Ayem Akpatuma’ bayan sun yada zango tsakanin Jalingo da Takum, inda suka samu nasarar cafke mutanen da ake zargi.
Wadanda suka shiga komar jami’an tsaron sun hada da Jaka Ejukun mai shekaru 24 da Peter Isaga mai shekaru 33 da Arachukwu Bedforth mai shekaru 2. Haka kuma rundunar ta tsallaka yankin Katsina Ala dake Jihar Benuwai, inda ta cafke Isaiah Suwe mai shekaru 23 da Amadu Barnabas Torba mai shekaru 23 sai Aondi mai shekaru 21. Sauran su ne, Nengenen Mbaawuaga Damian mai shekaru 22 da Aondoase Kayitor mai shekaru 18 da kuma Ternenge mai shekaru 19.
Duka mutanen tara, ana zarginsu ne da yin garkuwa da dan majalisar, Hon. Hosea Ibbi da kuma kisan sa. To amma an bayyana cewa daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Amodu Barnabas ne mutumin da fi kowa taka rawa wajen sace dan majalisar sannan ya kashe shi.