✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun cafke dan kasar wajen da ke taimaka wa ’yan ta’adda a Sakkwato

An dai kama shi ne a wani kauyen Jihar Sakkwato

Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta ce dakarunta da ke rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji sun cafke wani dan kasar waje da ya yi kaurin suna wajen aika wa ’yan ta’adda da bayanan sirri a kauyen Garuwa da ke Karamar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato.

Sojojin dai sun kama mutumin mai suna Jabe Buba ne ranar 21 ga watan Mayun 2022.

Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa maneMa labarai karin haske kan ayyukan dakarun sojoji a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce an sami nasarar ayyukan ne tsakanin ranar 19 ga watan Mayu zuwa biyu ga watan Yunin 2022.

A cewar Daraktan, an kuma sami wasu hotuna da bidiyo a wayar mutumin yana rike da bindigu a cikin daji, sannan an kwaci kudi Naira 130,000.

Kazalika, Manjo Janar Benard ya kuma ce sojojin sun kwato shanu 292 da kuma rakumi guda daya yayin wata karanbattarsu a kauyen Dampo da ke Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Ya kuma ce sun kwato mutum 152 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ’yan ta’adda 18, sannan suka kama wasu guda 25 a tsawon lokacin.

Daraktan ya kuma ce dakarun sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda tara da albarusai guda 100 da kuma shanun da aka sata guda 458 da babura 20. (NAN)