Sojoji sun yi wasu ’yan bindiga kwanton bauna inda suka kashe biyu daga cikinsu a Jihar Kaduna.
Sojojin Operation Thunder Strike sun kashe ’yan bindiga biyu yayin wani kwanton baunar da suka yi cikin dare a hanyar Gwagwada zuwa Chikun da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
- Yadda ’yan Najeriya ke caccakar Buhari kan satar Daliban Kaduna
- Yadda WhatsApp ya kwace mu daga ’yan bindiga —Daliban Kaduna
Aminiya ta gano cewa bayan ’yan bindigar a kan babura sun zo kusa da wurin da sojojin suke, da suka ga alamun yi mutu kwanton baunar, sai suka bude wuta a kokarinsu na wucewa.
Duk da haka sojojin suka shawo kansu suka kashe su yayin da sauran suka arce da raunukan harbi.
Kwamishinan Tsaro da Harkocin Cikin Gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa ya ce abubuwan da akwa kwato sun hdada gawarwakin, babur daya, bindiga kirar gida, wayar hannu, da tabar wiwi.
Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya taya sojojin murna kan nasarar da suka yi.