✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun aika ’yan bindiga lahira a Kaduna

Mai ba ’yan bindiga mafaka ko magani shi ma hukuncinshi daya da su

Dakarun sojin Najeriya sun aika wasu ’yan bindiga lahira bayan sun yi musu kwanton bauna a cikin daji a Jihar Kaduna.

Bayan samun rahoto kan take-taken ’yan bindigar ne sojojin Rundunar ‘Operation Thunder Strike’ suka yi musu kofar rago a hanyar Sabon Iche-Kagarko a daren Talata suka bindige su.

“’Yan bindigar na hanyarsu ta kai harin ne suka fada tarkon sojojin da suka bude musu wuta, su kuma suka mayar da martani.

“Bayan musayar wutar da ’yan bindigar da suka tsrere, sojoji sun tsinci gawar ’yan bindiga biyu sauran kuma ana zaton sun tsere ne da raunukan harbi; amma babu barnar da aka yi wa sojojin,” inji Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gidan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

Ya ce mazauna sun tabbatar cewa ’yan bindigar da aka kashe na daga cikin gungun wasu bata-gari da suka hana yankin sakat ne.

Aruwan ya kuma yi kira ga al’umma da kai wa jami’an tsaro rahoton duk wanda suka gani da raunin da basu gane ba, ko yake yi wa ’yan bindiga magani.

“Duk wanda aka samu yana ba wa ’yan bindiga mafaka kula yin jinyarsu to shi ma za a yanke amsa hukuncin dan bindiga.

“A kai rahoto ga cibiyar tsaro ta Jihar ta lambobin 09034000060, 0817018999 ko ta email: [email protected],” inji Aruwan.