✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun aika jagoran ’yan bindiga da wasu 3 lahira a Kaduna

Kwanan jagoran ’yan bindigar mai suna Dogo Bangaje da abokinsa ya kare ne a hannun sojoji a yankin Karamar Hukumar Giwa

Sojoji sun aika wani jagoran ’ya bindiga tare da wani na hannun damansa barzahu a Jihar Kaduna.

Kwanan jagoran ’yan bindigar mai suna Dogo Bangaje da abokin nasa ya kare ne a hannun sojoji a yankin Tumburku da ke Karamar Hukumar Giwa a karshen mako.

Sun gamu da ajalinsu ne bayan sojoji su yi arba da su a lokacin da suke neman tserewa, inda a yayin musayar wuta sojoji suka aika su lahira.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ta ce sojojin sun hallaka karin ’yan bindiga biyu a yankin Sabon Sara a karamar hukumar.

Aruwan ya ce sojojin daga rundunar Operation Whirl Punch sun kwato makamai da miyagun kwayoyi da wayoyi da magunguna da layu da kuma babur daga hannun ’yan ta’addan da suka hallaka.

Sanarwar ta ranar Litinin ta ce an hallaka karin ’yan ta’addan ne a wani wuri da suke jinyar marasa lafiya daga cikinsu, inda dakarun Suka lalata sansanin.

Gwamnan Kadunam Uba Sani da kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta 1, kuma Kwamandan Rundunar Operation Whirl Punch, Manjo-Janar MLD Saraso, sun jinjina wa dakarun bisa wannan namijin kokari.

Sun kuma bukace su da su ci gaba ragargazar ’yan ta’addan har sai sun ga bayansu.