✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Daba Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Kano

An tabbatar da rasuwar mutane uku a rikicin da ya barke a wurin taron gangi a Kano

A ranar Lahadi ne wasu mutane uku suka rasa rayuwarsu a wani rikicin da ya barke tsakanin wasu ’yan daba a unguwar Darmanawa da ke Karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano.

Rikicin ya faru ne bayan wani magidanci mai shekara 59 ya shirya taron gangi domin murnar auren ’ya’yansa.

Daga nan ne ’yan daba suka yi amfani da wannan dama don gwada kwanji.

Daga bisani abin ya rikide zuwa kazamin fadan da ya yi ajalin mutum uku.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an sanar da su cewa ana rigima a Darmanawa, sun aika jami’ansu inda daga bisani suka sami labarin cewa mutane uku sun rasa rayukansu.

SP Haruna ya bayar da tabbacin kama mutumin da ya shirya gangin da kuma wasu mutane biyu da ke anguwar.