✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Kama ’Yar Daba Mai Sa Kayan ’Yan Sanda A Neja

’Yan sanda a jihar Neja sun kama wata da ake zargin ’yar daba ce sanye da kayan sarki. Rundunar ’yan sandan jihar ta ce jami’anta…

’Yan sanda a jihar Neja sun kama wata da ake zargin ’yar daba ce sanye da kayan sarki.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce jami’anta sun kama matar ne yayin wani rikicin daba a Anguwan-Kadara da ke yankin Maitumbi na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun ya ce, sun kama wadda ake zargin dauke da wuka a lokacin da suke fadan.

“A ranar 10 ga watan Mayun 2024 da dare, jami’anmu da ke sintiri a Maitumbi suka samu bayanan sirri dangane da wata ’yar daba da ke sanya kayan sarki.

“Bayan bibiyar bayanan ne suka yi nasarar kama wata mata da ake zargi da yin sojan gona a Anguwan-Kadaram da ke Maitumbi,  tana sanya da rigar ’yan sanda da wata karamar wuka.

“An kuma same ta dauke da kunshin wani abu da ake zargin tabar wiwi ce da wasu muggan kwayoyi.

“A yayin da ake yi mata tambayoyi, ta ce ita mamba ce a wata kungiyar ’yan banga a Suleja, kuma wani ne ya kawo mata kayan ’yan sandan wanki, ita kuma sai ta gudu da su”.