✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji 6,199 da ke yaki da Boko Haram sun samu karin girma

Hafsan Hafsoshin Sojin Kasa, Laftana  Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da karin girma na musamman ga sojoji 6,199 da suke aiki da Rundunar Lafiya…

Hafsan Hafsoshin Sojin Kasa, Laftana  Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da karin girma na musamman ga sojoji 6,199 da suke aiki da Rundunar Lafiya Dole, wacce ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da Kakakin Sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman ya fitar ta ce Hafsan Hafsoshin Sojin Kasar ya amince ne da karin girman a ranar Talatar da ta gabata.

Jerin wadanda aka kara wa girman sun hada da Staff Saja zuwa Warrant Ofisa 329 da Saja zuwa Staff Saja 371 sai Kofur zuwa Saja 707 sai masu igiya daya zuwa Kofur 1,29o, yayin da kurata zuwa Kofur suka kai 3,502.

Birgediya Usman ya ce Hafsan Hafsoshin ya taya wadanda suka ci gajiyar karin girman murna kuma ya umarce su da su kara kokari don kawar da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Karin girman ya zo ne a daidai lokacin da rundunar ta Lafiya Dole da wadansu ’yan sibiliyan JTF suka kama wadansu ’yan Boko Haram hudu a kauyukan Kurnari da Nayinawa da ke wajen garin Damaturu a Jihar Yobe.

Mutanen da aka tabbatar ’yan Boko Haram ne sun hada da Bukar Waziri, mai shekara 25 da Mammade Lawan dan shekara 20, kuma an samu wani yaro mai suna Isah Muhammadu mai shekara 15 da mahaifinsa Muhammadu Damina mai shekara 40 da suka fito daga kauyen Talala.

Binciken farko ya gano cewa sun tsere ne daga wata maboyarsu da ke kauyen Talala da Buk a Karamar Hukumar Damboa a Jihar Borno, saboda yadda sojojin Najeriya ke fatattakarsu.

Rundunar ta Lafiya Dole ta kara zafafa yunkurin dakile masu kai hare-haren kunar bakin wake a Jihar Borno da suka sake bayyana a ’yan kwanakin nan, inda sojoji suka yin nasara a kan mata ’yan kunar bakin wake takwas da ake zargin Boko Haram ta aiko domin hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.