✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Soja ya harbe dan siyasa a cibiyar tattara sakamakon zabe

Majiyarmu ta ce a bisa kuskure sojan ya yi harbin

Wani soja ya harbe wani jigon Jam’iyyar PDP, Akinlabi Akinnaso, har lahira a Karamar Hukumar Idanre da ke Jihar Ondo.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda daya daga sojojin da aka tura samar da tsaro a cibiyar tattara sakamakon zabe a yankin ya harbi margayin bisa kuskure.

Majiyarmu ta ce hakan ta faru ne a lokacin da marigayin ya raka dan takararsu na Majalisar Wakilai da ya lashe zabe don karbar takardar shaidarsa a wajen INEC.

“Mun taru a cibiyar tattara sakamakon zabe muna jiran takardar shaidar lashe zabe ta dan takarnmu, Honorabul Akingbaso, a nan sojoji suka fara korar mu daga cibiyar don rage cunkoso.

“Bayan mun yi nesa da cibiyar, can sai muka hangi Akinnaso ya doshi cibiyar don ya cim mana alhali bai san abin da ke faruwa ba.

“Amma ko da ya yi kusa da sojojin sai muka ga ya fadi bayan da aka harbe shi.

“Bayan da muka dauke shi zuwa asibiti, aka tabbatar mana ya mutu,” in ji majiyar.

Da aka nemi jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce ba ta da cikakken bayani kan abin da ya faru.

Ta yi alkawarin za ta yi magana da zarar ta samu cikakken bayani kana bin da ya faru.