A ’yan kwanakin nan, wata sabuwar Kungiya ta samari masu dunkule hannu ta Najeriya (SMAN) ta bayyana tare da ci gaba samun karbuwa musamman a kafafen sada zumunta.
Samarin Najeriya ne dai suka kirkiri kungiyar domin su debe wa kansu kewa a kafafen na sada zumunta. Ko da yake a wasu kasashe ma akwai ire-iren wannan kungiya.
Yadda lamarin ya fara
Kungiyar Samari Marowata ta Zambia (SMAZ) wata kungiya ce da aka kirkira kuma ta yi tashe a kasar Zambia inda samari suka yi alkawarin ba za su ba ’yan matansu sama da kudin kasar K5 ba, sun gwammace su yi amfani da su wajen fara wata sana’a.
- Rufe makarantu: Daliban jami’a na barazanar dukan malamai
- Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano
Kafar yada labarai ta Zambian Observer ta rawaito cewa, an kama wani mai suna Mista Leonard Mweembe bayan ya lakada wa matarsa dukan kawo wuka saboda ta tambaye shi kudin kitso.
Matar dai ta tambaye shi kudin kitson ne amma ya shaida mata cewa shi yanzu mamba ne a kungiyar SMAZ, ba zai iya ba ta K15 ba sai dai K10.
“Lamarin fara kamar da wasa,” inji matar wadda ya ji mata rauni daga bisani aka garzaya da ita asibiti.
A watan Nuwamban 2020, jaridar Zambian Observer ta ruwaito cewa kungiyar ta tara kudi inda ta sayi wani jirgi mai cin mutane 800 domin kai mambobinta zuwa duka irin taron da suke so.
Dukkan kudaden kuma an tattara su ne daga adashin da mambobin kungiyar suka yi.
Kungiyar Samari Marowata ta Najeriya (SMAN)
SMAN dai kungiya ce da ta sha alwashin kankame hannu da kin kashe wa ’yan mata da ma duk wanda ke neman taimakonsu ko sisin kwabo.
Tun da batun ya fara jan hankali a intanet, samari da sauran mazan Najeriya sun rika nuna sha’awarsu ta shiga kungiyar.
Mutane da dama sun rika tambayar yadda za su shige ta, wasu kuma suka nuna katin kasancewarsu ’ya’yan kungiyar.
‘Zan ga abin da zan iya yi’
Taken kungiyar dai shi ne ‘Zan ga abinda zan iya yi’, kuma mambobinta kan nemo kowane irin uzuri a duk lokacin da budurwa da duk wani mutum ya nemi taimakonsu.
Baya ga taken kungiyar, ga wasu daga cikin hanzarin da mambobin kungiyar kan bayar a duk lokacin da wata budurwa ta tambaye su kudi:
- “Da ma kwanakin baya ki ka tambaye ni”
- “Ina tsammanin wasu kudade nan da mako mai zuwa”
- “Bari zan kira ki”
- “Zan neme ki”, da sauransu.
Yadda ake shiga kungiyar
Ga duk mai son shiga kungiyar, zai cike wani fom mai dauke da shaidar rantsuwa ta kungiyar kamar haka:
“NI…………NA YI ALKAWARIN KARE MUTUNCIN WANNAN KUNGIYA TARE DA SANIN YA KAMATA, CEWA BA ZAN BA DA KO SISIN KWABO DA SUNAN KOWANE IRIN TAIMAKO GA MATA BA.
ZAN GIRMAMA KUMA IN KARE TANADE-TANADEN KUNDIN TSARIN MULKIN WANNAN KUNGIYA MAI ALBARKA. ALLAH YA TAIMAKE NI.”
Ka’idojin kungiyar
Bugu da kari, ana bukatar mambobin kungiyar su kiyaye wadannan ka’idojin:
- Babu fita da ’yan mata, babu bikin murnar zagayowar ranar haihuwa.
- Idan ta ce maka, “Ina son ka” ko “Ina kewar ka”, kada ka ba ta amsa sai washegari.
- Idan ta tambaye ka kudi, ko ta ce ka tura mata N2,000 da sauri, ka kulle lambarta kuma ka goge ta.
- Kada ka kuskura ka ba ta kudin mota, kai ba ubanta ba ne.
- Ka kirkiri kiran waya na karya domin ka gudu idan ta gayyato maka kawarta yayin zuwa siyayya ko yawo.
- Kada ka yi mata tayin rage mata hanya a abin hawa, ka bar ta ta taka da kafarta ko ta hau motar haya.