✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sinadaran Soyayyar Ma’aurata

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo…

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga cigaban bayani kan ilmin soyayya inda a yau za mu tattauna kan sinadaran da suke gina soyayyar ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Sinadaran Soyayya
Ana lura da wasu muhimman abubuwa wajen fahimtar launi da ingancin soyayyar da ke tsakanin ma’aurata: wadannan abubuwa su ne kamar kayan hadin soyayya da ginshiki da kuma shika-shikan soyayya. Samunsu a kammalance a cikin soyayyar auratayya shi ke sa wannan soyayya ta zama cikakkiya kuma kammalalliyar soyayya; haka kuma rashin daya ko dukansu daga cikin dangantakar soyayya shi ke nuna nakasun wannan soyayya. Don haka ga bayani kan wadannan muhimman abubuwa don ma’aurata su fahimce su, su fahimci amfaninsu da kuma yadda za su inganta su cikin rayuwar aurensu, don ya kasance dangantakar soyayyarsu ta zama kammalalliya kuma cikakkiya.
1.    Shakuwa
Shakuwa na nufin kyakkyawar sanayya da sabo da suka kullu tsakanin mutum biyu ko sama da haka mai cike fahimtar juna da tsananin kulawa da kuma sadaukarwa. Mutum biyun da suka shaku sosai za ka tarar kodayaushe hankali da tunaninsu a hade yake, kuma suna ajiye da kyawawan shau’uka game da juna cikin zukatansu. Shakuwa wata aba ce mai kyawu kuma mai dadi, wacce ba ta baci ko ta lalace indai har an riga an yi ta; domin in ka ji wani ya ce ‘ai mun shaku sosai da wane,’ to yana nufin sun yi zaman jin dadi da kauna da kuma fahimtar juna.
Shakuwa na da wasu muhimman ginshikai da suke tallafarta, wadanda sai sun tabbata cikin danganta sannan ne za iya kiranta shakuwa, ga jerin abuwawan da ke haifar da sahihiyar shakuwa:
•    Tarayya
Kafin shakuwa ta kullu, sai ya kasance ana tare na wani muhimmin lokaci, kuma lokacin da ake taren nan, ana yawaita aiwatar da abubuwan rayuwar yau da kullum tare, ana yawan sabunta sanayya, ta hanyar yin ingantacciyar hira ta fahimtar juna da bayyanar da sirruka ga juna; ana fatan alheri ga juna, ana yin abubuwan faranta rai ga juna, ana taimako da kyautatawa ga juna.
Rashin yin tarayya cikin abubuwan yau da kullum na haifar da karancin shakuwa tsakanin ma’aurata, sai ga ka ma’aurata sun dade tare har sun hayayyafa, amma ba wata sahihiyar shakuwa tsakaninsu, saboda sun ware kansu ba su yin abubuwan yau da kullum tare, kowannensu harkar gabansa kadai yake yi, ba wanda ya san abin da dan uwan aurensa yake ciki, kila sai ibadar aure kadai suke yi tare, ko ita din suna yi ne a bukatance, ko kokarin ba da hakkin juna amma ba wata shakuwa cikinta. Yin abubuwa tare shi ne zai haifar da babban jigon shakuwa tsakanin ma’aurata.
•    Sabunta Sanayya
Shi ne yawan yin hira da tattaunawa game da kowane bangare na rayuwar juna, domin ta wannan hanya ce ma’aurata za su san tarihin juna, za su san komai da komai da ya faru a rayuwarsu: kanana da manya; masu muhimmanci da marasa muhimmaci; na farin ciki da na bakin ciki; tsofaffi da suka dade da sababbi na kwana-kwana nan. Domin dan Adam yana kara girma, hankalinsa da tunaninsa da sha’ukan cikin zuciyarsa na caccanzawa, da sun canza kuma dole halayyarsa da yanayin cudanyarsa da mutane ta canza. In ya kasance ma’aurata ba su sabunta sanayyarsu, wannan zai haifar da rashin fahimtar juna a tsakaninsu, wanda wannan wata babbar baraka ce da ke dakushe kaifin rayuwar aure ko ma ta kashe ta gaba daya.
•    Fahimtar Juna
Wannan shi ne babban jigo na shakuwa tsakanin ma’aurata, ya kasance sun fahimci junansu ta kowace fuska, ya kasance hankali, tunani da ra’ayoyinsu sun zamo daya a mafi yawan lokuta; sun san abubuwan so da kyamar junansu, sun fahimci yanayin halayya da sha’u’kan junansu; wannan zai taimaka masu kiyaye duk wani abu da zai kawo gardandami ko husuma tsakaninsu, kuma zai haifar musu da haduwar kai, yarda da aminta da juna.
•    Yarda
Wannan ita ce idan ma’aurata sun aminta da junansu a yadda suke ta kowace fuska, sun fahimci karfi da raunin junansu ta kowace fuska kuma sun aminta da haka, wani abu da ya yi rauni ko ya kasa a cikin halayya ko kasantuwar dayansu bai rage daraja da kimarsa ba a idon dayansu.
•    Haduwar Hankali da Tunani
Idan ma’aurata sun kasance yanayin hankalinsu sun hadu da juna, tunaninsu game da rayuwa ya zama daya, ra’ayinsu daya game da mafi muhimman al’amura cikin rayuwarsu, sannan bukatunsu da hangen da suke yi wa rayuwa ya zama daya, to wannan zai saukaka fahimtar juna tsakaninsu, kuma zai karfafa shakuwarsu.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allahu za mu ji bayani kan sauran kayan hadin soyayya. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.