Assalamu Alaikum; Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga misalan da a ga Allah daga daidaikun mata na wannan zamanin da fatan Allah Yasa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.
Farfesa Khalid Al ljubair wani babban likitan zuciya ya bad a wannan labari a daya daga cikin laccocinsa:
Ya ce na taba yin aiki ga wani yaro dan kimanin shekara 2 da rabi, a ranar Talata, Laraba yaron ya fara jin sauki. Ran Alhamis da misalin karfe 11:15 na safe ban taba mancewa saboda yadda abin ya girgiza ni. Daya daga cikin Nas-Nas ta sanar da ni numfashin yaron ya dauke. Wajen minti 45 na dauka ina famar tayar da zuciyarsa ta fara bugawa amma ina!
Sai can daga baya Allah Ya kaddara zuciyar ta fara bugawa muka yi masa godiya. Na je don sanar da iyayensa hadarin da yake ciki, wannan abu shi ya fi kowanne wahala ga likita amma ya zama dole. Na dudduba ban ga babansa ba, sai na ga mahaifiyarsa sai nake sanar da ita zuciyar yaron ta tsaya ne saboda barkewar jini a makogwaronsa wanda ba mu san asalinsa ba kuma muna fargabar ko kwakwalwarsa ta shanye. Yaya kuke zaton wannan baiwar Allah za ta yi a wannan lokaci? Ta barke da kuka! Ko ta dora min laifin? Ko daya ba ta yi ba sai dai kadai ta ce alhamdulillah. Ta tafi ta bar ni.
Bayan kwanaki goma yaron ya farfado har ya fara motsi, muka yi wa Allah godiya ganin kwakwalwarsa ta fara farfadowa. Bayan kwanaki 12 zuciyar ta kara tsayawa kamar wancan lokaci dai. Amma wannan karon har bayan minti 45 dai zuciyar ba ta buga ba, na sanar da mahaifiyarsa cewa da kyar zai tashi kuma. Sai dai kawai ta ce “Alhamdulillah, Ya Allah in akwai alheri ga samun lafiyarsa to Ka ba shi lafiya Ya Ubangijina!”
Cikin ikon Allah zuciyarsa ta ci gaba da aiki kuma. Sai da irin haka ta faru sai 6 kafin kwararren likita a fannin hanyoyin da iska ke bi ya yi masa aikin da ya tsayar da barkewar jini a zuciyarsa ta koma aiki yadda ya kamata. Bayan wata 3 da rabi, yaron yana samun sauki amma bai fara motsi ba, yana fara motsi kuma sai aka jarrabce shi da wani katon kurji mai cike da ruwa a saman kansa irin wanda ban taba gani ba. Na sanar da mahaifiyarsa wannan babbar matsala sai dai ta ce “Alhamdulillah” kawai ta yi tafiyarta. Nan da nan muka mai da shi bangaren kwakwalwa na asibitin suka ci gaba da duba shi. Bayan mako 3 ya samu lafiya daga kurajen amma har yanzu bai fara motsi ba. Bayan mako 2 kuma ya samu gurbacewar jini zafin jikinsa ya yi sama sosai har sai da ya kai ma’aunin 41.2C. Haka dai na kara sanar da mahaifiyarsa wannan mawuyacin halin da ya sake shiga, sai dai kawai ta ce, cikin yanayi mai cike da hakuri da sakankancewa: “Alhamdulillah, Ya Allah in akwai alheri ga samun lafiyarsa to Ka ba shi lafiya ya Ubangijina!”
Bayan na bar ta a gado mai lamba 5 sai na je gado mai lamba 6 na samu mahaifiyar yaron da ke kan gadon tana kuka tana ihu tana ce min Likita! Likita! Ka yi wani abu, zafin jikinsa ya haura har 37.6! Mutuwa zai yi! Mutuwa zai yi!” Na ce da ita cike da al’ajabi: “Dubi waccan uwar mana ta gado na 5, zafin jikin danta ya kai 41C amma ta yi hakuri godiya take ga Allah? Sai ta ce:” Wannan matar a mace take ba ta jin komai.” A wannan lokaci na tuna Hadisin Manzon Allah (SAW): “Albarka ta tabbata ga baki.” A shekara 23 na aikin asibiti ban taba ganin mace mai hakuri irinta ba. Muka ci gaba da kula da shi har tsawon wata 6 da rabi. Har ya fita daga wannan bangaren amma bai magana, bai gani bai ji bai motsi da kuma kirjinsa a bude har kana iya ganin zuciyarsa tana bugawa. Mahaifiyarsa ta ci gaba da canja masa bandeji a kai-a-kai kuma ta ci gaba da yin hakuri da kyakykyawar fata.
Bayan wata 2 da rabi yaron gaba daya ya samu lafiya cikin rahamar Ubangiji da kuma lada ga wannan baiwa mai kankan da kai. Sai ga shi yana tsere wa mahaifiyarsa da kafafunsa kamar dai ba abin da ya taba samunsa Labarin ba nan ya kare ba, abin da ya girgiza ni ya sa idanuwana suka cika da kwalla, shi ne abin da ya biyo baya:
Sai mako na gaba za mu karasa labarin tare da darussan koyi ga Uwargida daga cikinsa. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarslSa a koyaushe, amin.