Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC a Jihar Kano sun kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne.
Kakakin rundunar, Ibrahim Abdullahi, ya sanar a ranar Laraba cewa an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Fagge ta jihar ranar Talata.
- Mun gano masu shirin wargaza bukukuwan mika mulki —DSS
- Gwamnatin Kano ta wanke Alhassan Doguwa daga zargin kisan kai
Sanarwar ta bayyana cewa, “Sun kasance suna gudanar da ayyukan ta’addanci a kusa da Sabon Gari, cikin karamar hukumar Fagge inda suke kwace wayoyin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”
Kakakin ya bayyana cewa jami’an hukumar na leken asiri ne suka gano barayin, inda ya jaddada hukumar na ci gaba da yaki da duk wani nau’in aikata laifuka a jihar.
A baya-bayan nan ana kara samun karuwar matsalar fashin waya a cikin birnin Kano, amma ya tabbatar da aniyar hukumar na dakile wannan lamari.
Ya bayyana cewa, a ranar Talata wasu fusatattun mazauna garin suka kone wani babur mai uku da ake zargin wasu masu kwace waya ke amfani da shi.