Shugabannin Kananan Hukumomi bakwai na jam’iyyar PDP a jihar Ekiti sun koma jam’iyyar APC, shugabannin sun sauya jam’iyyar ne lokacin da suka karbi bakoncin Gwamnan jihar Kayode Fayemi da ke cikin jam’iyyar APC.
Bayan sauya shekar da shugabannin suka yi sun bayyana Gwamnan jihar a matsayin shugaba nagari wanda bai nuna banbancin siyasa tun lokacin da ya fara jan ragamar jihar.
Shugabannin Kananan Hukumomin sun hada da: Ayodeji Daniel ( Ekiti ta Yamma), Abiodun Dada (Ijero), Yemi Ayeni (Ikere), Tunde Aladegbami (Ido/Osi), Sikiru Ogundana (Ekiti ta Gabas), Olubayode Okeya (Emure), da Yemi Owoeye (Efon).