Gwamnoni da sarakunan yankin Arewa sun yi watsi da ƙudirin dokar ƙara haraji da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar dokoki ta ƙasa.
Sun yi fatali da ƙudurin dokar, musamman batun ƙarin harajin VAT zuwa 10%, da cewa zai cutar da yankin Arewa da gwamnatocin jihohi.
A wani taro da suka gudanar kan matsalolin da suka dabaibaye Arewa, shugabannin yankin sun buƙaci a gaggauta gyara wutar lantarkin yankin da lalace sama da kwanaki takwas da suka gabata.
Sun bayyana cewa kwanaki 10 da aka shafe babu wuta a yankin babbar barazana ce ga al’ummarsu.
Don haka suka bukaci a samar da sabbin layukan tura wuta zuwa yankin, wanda shi ne ƙashin bayan noma da samar da abinci a ƙasar.
Taron nasu wanda Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya halarta, ya tattauna kan matsalolin tsaro da ilimi da tattalin arziƙi da suka yi wa yankin katutu.
A ranar 3 ga watan nan na Oktoba ne Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisa ƙudurin wanda Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen ya karanta.
Tinubu ya bayyana cewa kuɗurin zai haɗe dokar harajin Nijeriya ta 2024, kuma zai samar da gyara a tsarin karɓar haraji na ƙasa da dokar kula da haraji, tare da samar da tsayayyen tsari na shari’a ga duk wani haraji a Nijeriya tare da rage saɓani.
Sauran sun hada da dokar kafa Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Nijeriya, wadda za ta soke dokar Hukumar Tata Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kuma dokar kafa Hukumar Tattara Haraji ta Haɗin Gwiwa, wadda za ta kafa kotun sauraron ƙararrakin haraji da kuma naɗa mai kula da haraji.
Tinubu ya ce an tsara kudirin ne don tallafa wa manufofin gwamnatinsa da kuma ƙarfafa cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar.
Ya ce, “fa’idodi ƙudurin sun haɗa da bunƙasa tattalin arziki ta hanyar inganta biyan haraji da ƙarfafa cibiyoyin hada-hadar kuɗi da samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai inganci,” in ji shi.
Da yake bayyana matakinsu na ƙin amincewa da ƙudirin, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce: “Wannan ya faru ne saboda kamfanoni za su riƙa biyan harajin VAT ne a inda hedikwatarsu take, ba a inda suke aiki ba.
“Saboda haka, mun yi watsi da shirin gyaran harajin, muna kuma kira ga majalisar dokoki ta ƙasa da ta yi fatali duk wannan ƙudiri da zai kawo cikas ga rayuwar al’ummarmu.
“Don kauce wa shakku, Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ba ta ƙyamar duk wata manufa ko shiri da zai tabbatar da ci-gaban ƙasa.
“Duk da haka, muna kira da a yi adalci da daidaito wajen aiwatar da dukkan manufofi da tsare-tsare don tabbatar da cewa babu wani yanki na da zai mamaye shi ko kuma a ware shi”, in ji kungiyar.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin, ya ci gaba da cewa matsalar tattalin arzikin da ’yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu ta fi muni a Arewa fiye da yankin Kudu saboda abin da ya kira “bambamci na rashin daidaiton tattalin arziki.”
Ya ci gaba da cewa: “Bisa la’kari da halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki a yanzu, muna kira ga ’yan Nijeriya su kwantar da hankulansu, domin jihohi da gwamnatin tarayya suna bakin ƙoƙarinsu wajen aiwatar da matakan da za su dakile illar wahalar.”
Gwamnan ya bayyana cewa zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a watan Agusta jan hankali ne ga dukkan shugabannin Arewa.
A cewarsa, rashin aikin yi tsakanin matasa abin damuwa ne, wanda jahilci, talauci, da rashin samun damammakin tattalin arziki ke haifarwa.
Manyan sarakunan da suka suka halarci zaman da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna sun haɗa da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garba Al- Amin El-Kanemi da Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli.
Sauran su ne Malam Ahmad Nuhu Bamalli; Ohinoyi na Ƙasar Ebira Alhaji Ahmed Tijani Anaje da Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu da Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da Sauransu.