✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugabancin APC: Ana zargin Sanata Sheriff da hada baki da PDP

Ana zargin Sheriff zai hada baki da PDP idan ya zama shugaban APC na kasa.

Ana zargin tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali-Modu Sheriff, wanda ke neman Shugabancin Jam’iyyar APC, da hada baki da jam’iyyar adawa ta PDP idan bukatarsa ta biya.

A wani sauti da aka nada da ya karade gari, an ji mambobin Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar PDP suna fatar ganin Sanata Sheriff ya zama Shugaban ACP na kasa.

An kuma ji su suna cewa idan har Sheriff ya zama Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa kafin babban zaben 2023 to PDP za ta tsinci dami a kala.

Sai dai wata sanarwa da Kungiyar Yakin Neman Zaben Sanata Ali-Modu Sheriff (SASCO) ta fitar ta hannun Sanata Victor Lar, ta ce yi watsi da zargin.

A cewar kungiyar sakon muryar ba komai ba ne face makircin wasu mahassada daga jiharsa, wadanda ya ce daukakar da ya samu a siyasa ta tsone musu ido.

“Muna tabbatar wa ’yan Najeriya cewa da izinin Allah sai kuma goyon bayan mambobin jam’iyya, idan Sheriff ya zama Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, zai yi aiki da gaskiya ba tare da kullatar kowa ba ko la’akari da bambancin kabila ko addini,” inji sanarwar da Sanata Victor Lar ya fitar.

Tuni dai Sheriff ya bukaci gwamnonin jam’iyyar APC da mambobin jam’iyyar da su yi wasti da sakon muryar a matsayin wata manakisa da aka shirya masa domin dakile shi a siyasance.