Shugaban Ƙasar Vietnam, Vo Van Thuong ya yi murabus shekara guda bayan hawansa mulkin ƙasar da ke karkashin ikon masu ra’ayin gurguzu.
Tuni dai Majalisar Dokokin Vietnam ta amince da murabus ɗin Van Thuong mai shekaru 53 a duniya, inda aka bai wa mataimakiyarsa riƙon ƙwarya.
- Majalisa ta amince da ƙudirin yi wa Alƙalai ƙarin albashi
- Tinubu Ya Roƙi ’Yan Majalisa Su Tsagaita Gayyatar Shugabannin Ma’aikatu
Murabus ɗin Van Thuong na zuwa ne a daidai lokacin da Vietnam ta faɗa cikin rikicin siyasa bayan ajiye aiki da magabacinsa ya yi tare da korar wadansu ministoci da shugabannin ma’aikatu kan zargin badaƙala da dukiyoyin gwamnati.
An dai naɗa mataimakiyarsa, Thi Anh Xuan a matsayin shugabar rikon kwarya, kafin a samu wanda zai maye gurbinsa kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin kasar ya tanada.
Shi dai Vo Van Thuong ya hau kan gadon mulkin kasar Vietnam ne a ranar biyu ga watan Maris na 2023.
Van Thuong ya karɓi ragama ne bayan murabus din ba-zata da magabacinsa, Nguyen Xuan Phuc ya yi, inda ya yi alkawarin samar da sauye-sauye don sake saita tafiyar kasar.
Vietnam dai na fama da matsalar cin hanci da rashawa da ta babaibaye ma’aikatun gwamnati, lamarin da ke hana ruwa gudu wajen ci gaban kasar da a shekarun baya ta share lokaci mai tsawo tana yaƙi da Amurka.