✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban ’yan banga a Kaduna ‘dan bindiga ne’ —Sojoji

Dubun shugaban ’yan bangar Rigasa ta cika bayan dan bindiga ya tona mishi asiri

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta kama shugaban ’yan banga na yankin Rigasa a Jihar Kaduna kan zargin hada baki da ’yan bindiga da kuma hannunsa a hare-hare gami da garkuwa da mutane a yankin.

Daraktan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaron, Birgediya-Janar Benard Onyeuko, ne ya sanar da haka, a lokacin da yake shaida wa manema labarai cewa tuni aka kama shugaban ’yan bangar.

Birgediya-Janar Onyeuko ya ce sojojin Rundunar Thunder Strike da Rundunar Whirl Punch, sun cafke shugaban ’yan bangar ne a unguwar Paka da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba, 2021.

”A lokacin aikin, sojoji sun dakile tare da cafke masu aikata miyagun laifuka suka kuma kwace makamai a hannunsu,” inji shi.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa dubun shugaban ’yan bangar ta cika ne bayan wani kasurgumin dan bindiga da sojoji suka kama ya shida musu cewa shugaban ’yan bangar Rigasa na daga cikin masu taimaka wa harkokinsu a yankin.

“A ranar 3 ga Disamba, 2021, sojoji suka kama wani kasurgumin dan bindiga a kauyen Paka da ke Karamar Hukumar Igabi, wanda ya shaida musu cewa Shugaban ’Yan Banga na Rigasa na taimaka wa ’yan bindiga kuma yana da hannu a wasu hare-hare da garkuwa da mutane da aka yi a yankin,” kamar yadda ya bayyana.