Daraktan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaron, Birgediya-Janar Benard Onyeuko, ne ya sanar da haka, a lokacin da yake shaida wa manema labarai cewa tuni aka kama shugaban ’yan bangar.
- Mutanen ake zargi da kashe Kwamishina a Katsina sun shiga hannu
- Abin da ya sa muka bude layin waya a Katsina —Masari
Birgediya-Janar Onyeuko ya ce sojojin Rundunar Thunder Strike da Rundunar Whirl Punch, sun cafke shugaban ’yan bangar ne a unguwar Paka da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba, 2021.
Ya shaida wa ’yan jarida cewa dubun shugaban ’yan bangar ta cika ne bayan wani kasurgumin dan bindiga da sojoji suka kama ya shida musu cewa shugaban ’yan bangar Rigasa na daga cikin masu taimaka wa harkokinsu a yankin.
“A ranar 3 ga Disamba, 2021, sojoji suka kama wani kasurgumin dan bindiga a kauyen Paka da ke Karamar Hukumar Igabi, wanda ya shaida musu cewa Shugaban ’Yan Banga na Rigasa na taimaka wa ’yan bindiga kuma yana da hannu a wasu hare-hare da garkuwa da mutane da aka yi a yankin,” kamar yadda ya bayyana.