✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban PDP na Zamfara, Sani Ahmad, ya rasu

Ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, Dokta Sani Ahmad, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Mukhtar Lugga ne ya tabbatar da rasuwar marigayin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Gusau, babban birnin jihar, ta wayar salula.

Lugga ya ce rashin lafiyar da ta yi ajalin marigayin takaitacciya ce, saboda ko a ranar da zai rasu, sai da ya gana da Majalisar Malamai ta Jihar a Gusau.

Ya ce an tabbatar da rasuwar marigayin ne bayan da aka dauke shi zuwa asibiti bayan da jikinsa ya yi zafi.

Marigayin ya rasu yana da shekara 62, kuma ya bar mata biyu da ‘ya’ya shida.

A ranar 23 ga watan Satumba aka zabi marigayin a matsayin shugaban PDP na Zamfara bayan murabus da Kanal Bala Mande  ya yi

(NAN)