✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban PDP na Kano ya bukaci shugaban jam’iyyar na kasa ya yi murabus

Yi wa yankin Kudu adalci shi ne Iyorchia Ayu ya cika alkawarin da ya dauka na ajiye mukaminsa.

Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, ya nemi shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da ya cika alkawarin da ya dauka na ajiye mukaminsa.

Sagagi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban ofishin jam’iyyar da ke birnin Dabo a Yammacin Talata.

A cewar Sagagi, shugaban jam’iyyar na kasa ya yi alkawarin cewa zai yi murabus idan aka tsayar da dan arewa a matsayin dan takarar Shugaban Kasa domin bai wa yankin Kudu dama.

“To yanzu an tsayar da dan Arewa ya kamata ya mutunta wannan yarjejeniya, saboda su ma jama’ar Kudu su samu nutsuwar zabar mu”.

Ya kara da cewa “Ɗan takarar shugaban Kasa daga Arewa, Shugaban jam’iyya daga Arewa, shugaban Kwamitin Amintattun jam’iyya shi ma daga Arewa, Shugaban gwamnonin jam’iyya shi ma daga Arewa, to kuwa ci gaba da tafiya a hakan ba adalci ba ne ga ’yan Kudu.”

Sagagi ya nanata cewa, shugabannin PDP a Kano sun tabbatar da mubaya’a da biyayyarsu ga uwar jam’iyyar, kuma ba su da alaka da kowace jam’iyya idan ba PDP din ba.

Ya kara da cewa, sun yi daura damarar tallata dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da sauran wadanda jam’iyyar ta tsayar.

Dangane da barakar da jam’iyyar ke fama da ita a Kano, Sagagi ya ce suna ci gaba da tattaunawa domin neman hadin kan sauran ’ya’yan jam’iyyar wajen ganin an cimma burin da aka saka a gaba.