Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Murktar Bajeh, ya yi murabus daga mukaminsa domin nuna adawa da zargin ta’addanci da ake masa da abokansa.
A ranar 23 ga watan Maris ne gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya bayyana tara daga cikin mambobin majalisar 25 a matsayin ’yan ta’adda, bisa zargin su da hannu a zaben ’yan majalisar dokokin da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Maris.
Bello ya bukaci majalisar ta wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar, Mista Matthew Kolawale, da ta dakatar da mambobin tara da suka hada da shugaban masu rinjayen, tare da bincikar ayyukansu a lokacin zaben ’yan majalisar.
Amma Bajeh, a wata wasika da ya aike wa majalisar, ya sanar da kudurinsa na sauka daga mukamin shugaban masu rinjaye.
Shugaban majalisar wanda ya karanta wasikar Bajeh a zauren majalisar, ya nemi jin ta bakinsa kan lamarin.
A lokacin ne mataimakin shugaban majalisar, Alfa Momoh-Rabiu, ya gabatar da kudirin nadin wanda zai maye gurbin shugaban masu rinjaye, Mista Ahmed Dahiru, wanda zai maye gurbin Bajeh a matsayin shugaban masu rinjaye.
Kakakin majalisar, ya yi gaggawar tambayar ’yan majalisar, kan batun nadin shugaban masu rinjaye na majalisar, inda suka amince da Dahiru a matsayin sabon shugaban masu rinjaye.