Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) reshen Jihar Zamfara Kwamared Bashir Muhammad Marafa ya sauka daga mukaminsa.
Marafa ya ce ya dauki matakin ne domin ci gaban kungiyar da ma jihar baki daya.
- ’Yan kwadago sun dakatar da yajin aiki
- Za a debi mutum 7,500 aikin dan sanda a jihar Zamfara
- Gwamnatin Zamfara ta tsayar da ranar zaben kananan hukumomi
- Za a fara rataye masu tukin ganganci a Zamfara
Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su ba wa kungiyar hadin kai tare da ci gaba da gwagwarmayar kwatar hakkokinsu da aka tauye.
Ya bayyana cewa kafin yin murabus dinsa sai da ya tuntunbi uwar kungiyar ta NLC kuma ta amince da hakan.
Marafa ya musanta zargin da ake samuwar rikici a kungiyar wanda wasu ke ganin shi ne musabbabin yin murabus dinsa.
Tuni dai masu ruwa da tsaki na NLC reshen jihar suka maye gurbinsa da Kwamared Sani Halliru Kurya a matsayin sabon shugaba a jihar.
Idan ba a manta ba a baya-bayan ne aka ba wa mataimakin Shugaban NLC na jihar, Bello Galadima Maguru mukamin Mai ba Gwamna Shawara kan harkar Kwadago a jihar.